Monday, 12 March 2018

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson na ziyara a Abuja

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya isa Abuja babban birnin Najeriya, a ziyararsa ta farko zuwa kasar. Ziyarar dai wani bangare ce ta rangadin da yake zuwa kasashen Afirka shida, da nufin tsaurara tsaro da kulla dangantakar kasuwanci.


A yayin ziyarar tasa Mista Tillerson zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari inda ake sa ran za su tattauna batutuwan da suka hada da na yaki da ta'addanci da batutuwan da suka shafi ayyukan jin kai a arewa maso gabashin Najeriya da kuma yankin Tafkin Chadi.

Ana kuma sa ran za su amince a kan yadda za a kara samar da zaman lafiya da tsaro a yankin Naija Delta, da kuma gano hanyoyin da kasashen biyu za su amfana da juna ta fuskar kasuwanci da zuba jari.

Mista Tillerson dai yana ziyarar mako daya ne a Afirka.

Ya ziyarci yankin kusuwar Afirka kwanaki kadan bayan da ya sanar da bayar da sabon tallafi na dala miliyan 533 ga Afirka, inda a ciki aka ware dala miliyan 128 ga Najeriya da kasashen da suke makwabtaka da yankin Tafkin Chadi.

Ziyarar dai tana zuwa ne shekara guda bayan da Shugaba Donald Trump ya karbi mulki daga hannun Barack Obama.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment