Monday, 19 March 2018

Salah zai iya maye gurbin Messi da Ronaldo>>Klopp

media
Mai horar da Liverpool Jurgen Klopp ya ce yana sa ran nan gaba dan wasansa Mohammed Salah, zai iya nun bajintar da ta zarta wadda Lionel Messi ya nuna.

Klopp ya bayyan haka ne bayan kammala wasa tsakanin Liverpool da Watford wanda suka lallasa takwarorin nasu da 5-0 kuma Salah ne ya ci kwallaye 4 daga ciki.
Hakan ya bai wa Salah damar ci wa kungiyarsa ta Liverpool jimillar kwallaye 36, mafi yawa da wani sabon dan wasa kungiyar ya ci mata a shekarunsa na farko.
Mai horar da Liverpool ya ce yana da kwarin gwiwar Salah mai shekaru 25, yana da damar maye gurbin Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a matsayin gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya.
rfihausa.

No comments:

Post a Comment