Thursday, 29 March 2018

Sanatocin Najeriya sun hana El-Rufai karbar bashin $350m

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da bukatar da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gabatar mata ta cin bashin $350m daga Bankin Duniya. 'Yan majalisar sun dauki matakin ne bayan wani kwamiti da Sanata Shehu Sani ke jagoranta ya gabatar musu rahoto kan batun.


A shekarar da ta wuce ne gwamnatin jihar Kaduna ta mika bukatar neman bashin domin gudanar da ayyukan 'ci gaban kasa'

'Yan majalisarsun yi watsi da bukatar karbo bashin ne "saboda Kaduna ita ce jiha ta biyu da ta fi yawan bashin da ake bin ta".
bbchausa.

No comments:

Post a Comment