Thursday, 15 March 2018

Sauke sakataren Amurka, Tillerson bazai shafi Najeriya ba>>Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa cire sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Tillerson daga aiki da shugaban kasar, Donald Trump yayi kwana daya bayan da ya kawo ziyara Naijeriya bazai shafi dangantakar kasashen biyu ba, ministan harkokin waje, Geoffrey ne ya bayyanawa manema labarai haka, jiya Laraba bayan kammala taron majalisar koli ta kasa.


Geoffrey ya bayyana cewa ita kasa tana cigaba da aiki a koda yaushe, kuma a lokacin da Tillerson ya kawo ziyara Najeriya, kasar Amurkace ke magana kuma duk wata magana da aka yi dashi ba zata tashi ba domin a hukumance yana maganane a madadin kasarshi.

Bayan da aka sauke Tillerson dai wasu sun rika barkwanci da abin, inda har sanata Ben Bruce ke cewa irin matsalar rashin aikin yi da ake da ita a Najeriya ta shafi sakataren harkokin wajen Amurkar dan gashi kwana daya da ziyarar da ya kawo Najeriya shima ya ra sa aikinshi.

Sanata Shehu Sani ma yayi barkwanci da cire Tillerson din inda yace ya bar tsintsiya ya kuma je ya iske tsintsiya.

No comments:

Post a Comment