Thursday, 8 March 2018

Shahararren Marubucin Kasar Hausa, Abubakar Imam

Imam wanda aka haifa a garin Kagara dake jihar Neja, an haife shi a shekarar 1911 kuma  shine editan jaridar Hausa ta farko mai suna GASKIYA TAFI KWABO kuma ya wallafa littafai da dama irinsu Ruwan Bagaja, Magana Jari ce, Karamin Sani Kukumi da tarihin Annabawa da dai sauransu.


Imam wanda ya taka rawar gani wajen cigaban harshen Hausa, ya bar duniya a shekarar 1981 amma duk da baya nan, ana ci gaba da amfani da wallafe-wallafensa wajen bunkasa harshen Hausa, wanda masana na ganin har yanzu ba a samu kamar sa ba cikin jinsin maza, wajen iya rubuta kagaggen labari.

Masanan na ganin tun bayan Abubakar Imam ba a samu mai maye  gurbinsa ba cikin jinsin maza wajen iya rubuta kagaggun labarai.

Sanin kowa ne a yanzu mata sun fi maza hazaka wajen iya rubuta kagaggen labari, wanda hakan ya sa sasshen hausa na  BBC saka wata gasa ta mata zalla mai suna "HIKAYATA" kuma aka samu mata da dama wadanda suka lashe wannan gasar.

Hakan ya sa wancan lokacin aka yi wa shugaban sashen Hausa na BBC wato Jimeh Saleh tambaya dalilin da ya sa ba su saka maza cikin wannan gasar ba?

Inda nan take Jimeh ya yi sharhi kuma ya nuna mata sun fi maza iya rubuta kagaggen labari. Wanda yana ganin maza za su iya amma fa da wuya ganin an baro maza tun  a labarin Dantsuntsu wato Magana Jari ce, na Abubakar Imam.

Ma'ana tun bayan Abubaka Imam babu wani na miji da ya yi suna wajen rubuta kagaggen labari.

Shim taya maza za su farka daga barci, wajen rubuta kagaggen labari?

Ya kamata malaman makaranta su kara zage dantse wajen koyawa yara musamman maza yadda ake rubuta labarai tun a firamari da sakandare, haka kuma ya kamata gwamnati da 'yan kasuwa da kungiyoyi masu zaman Kansu su yi koyi da BBC wajen saka ire-iren wadanan gasar don  bunkasa harshen Hausa.
rariya

No comments:

Post a Comment