Monday, 12 March 2018

Sheikh Ahmad Gumi yayi Allah wadai da hotunan badala na bikin diyar Ganduje: Ya gargadi mutanen Kano da su guji fushin Allah

A karin farko tun bayan da hotunan bikin diyar gwamnan jihar Kano da dan gwamnan jihar Oyo, Fatima Ganduje da Idris Ajimobi suka jawo cece kuce a tsakanin Al-Umma an samu malamin addini da ya fito fili yayi Allah wadai da wannan abu. Sheikh Dr. Ahmad Gumi yace abinda ya faru a bikin 'ya'yan gwamnonin ya bata mishi rai.


Kamar yanda Premium Times ta ruwaito, a karatun da malamin yake yi na sati-sati, ya bayyana cewa irin rugume-rungumen da 'ya'yan gwamnonin suka yi a bainar jama'a  abin kunyane suka jawowa addinin mulunci da ma tarbiyyar mutanen Arewa.

Sheikh Gumi ya tambayi cewa shin ina askarawan Hisba suke ne irin wannan abu yake faruwa, shima ya kawo misalin abinda ya faru da Rahama Sadau inda yace, a jihar da aka hukunta wata jarumar fim din Hausa dan ta rungumi mawaki kuma aka samu diyar gwamna ta yi irin wannan abu, hakan na nuna cewa zasu halatta yin wannan badala kenan. Ya kara da tambayar cewa shin irin shuwagabbanin da muka zaba kenan?.

A karshe dai Sheikh Gumi ya gargadi mutanen Kano ta cewa suji tsoron Allah kada fushin Allah ya afka musu, inda ya bayar da misalin abinda ke faruwa a jihar Borno.

Dama dai tun bayan da wannan abu ya faru na diyar gwamnan ake samun mutane suna tambayar ina malamanmu na Arewa, babu wanda ya fito yayi Allah wadai da wannan abu, musamman Hukumar Hisba ta Kano, wasu sun rika tambayar shin wai ina Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa?, amma a jiyan Malam Daurawa ya basu amsa.

No comments:

Post a Comment