Monday, 12 March 2018

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya baiwa masu kiranshi da yayi magana akan hotunan bikin diyar gwamnan Kano amsa

Bayan da hotunan auren diyar gwamna  jihar Kano, Fatima Abdullahi Umar Ganduje da Angonta, dan Gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi suka bayyana suna sumbatar junansu abin ya dauki hankulan mutane har wasu suka rika kiran cewa ina malamai masu wa'azi idan 'ya'yan talakawa sukayi ba daidai ba?. Kai tsaye wasu suka rika kiran sunan Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa suna cewa ya suka ji yayi shiru akan wadannan hotunan?. To malam dai ya basu amsa.


Ga abinda malam ya bayyana kamar haka:
"INA DAURAWA?

 tambaya ina Daurawa?

Amsa:
Ranar Asabar bayan a Daura aure kamar karfe daya 
Na kama hanya zuwa sokoto domin bitar littafi da Dr Mansur ya rubuta akan sharhin iziyya, bayan nayi kwana biyu, nazo Zamfara nayi waazi na kwana daya, daga nan na wuce Kaduna nayi program a DITV na awa biyu.
Ranar Juma'a nayiwa mata waazi a Rigasa daganan na wuce masallaci nayi free kudubah
Kuma na gabatar da khudubar juma'a. 
Bayan magariba nayi waazi a masallacin Shaik Rabiu Daura.

Ranar Asabar da safe nayiwa mata waazi a masallacin Sultan Bello.
Daga nan na taho Kano.
Masu son su ganni na dawo Ina office.

Bayan abubuwan da suka faru a wajan bikin yar Gov kowa yana jira yaji mai Daurawa zai fada, to ku mai kuke zaton zan fada?".

No comments:

Post a Comment