Tuesday, 20 March 2018

Shin ko kun san garin da kusan kowa ke tallan asuwaki?

Bisa tarihi dai, kowanne gari da sana'ar da ya shahara a kai wadda kuma galibi al'umarsa ke dogaro da ita. A kauyen Abokim, da ke karamar hukumar Etung a jihar Cross-River ta kudancin Najeriya, baya ga noma wanda shi ne gadon al'ummomin Afirka da dama, jama'ar kauyen, maza da mata manya da yara, babu sana'ar da suke yi kamar sana'ar ferewa da kuma tallan asuwaki ko magogi.


A kwanakin baya, wakilin BBC, Is'haq Khalid, ya ziyarci kauyen, inda ya kuma tattauna da wasu masu wannan sana'a.

Wakilin BBC, ya ce wasu masu wannan sana'a sun shaida masa cewa, shaharar wannan sana'a ta kai ga har jama'a daga wasu kasashen Afirka musamman Jamhuriyar Benin na zuwa garin wanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru domin sarin asuwakin buhu-buhu zuwa kasashensu.

To sai dai kuma rikicin 'yan aware da ake yi a yankin Kamaru mai magana da harshen Ingilishi, inda ake sayo itacen da ake ferewa domin yin magogin, ya fara kawo cikas ga sana'ar a garin na Abokim da ke kan iyaka.

Fatan jama'ar wannan yanki dai shi ne, sana'ar tasu ta kara bunkasa domin su samu karin kudin shiga, sannan ita ma Najeriya, ta kasance mai alfahari da fitar da magogi kasashen duniya don bunkasa tattalin arzikinta.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment