Tuesday, 20 March 2018

Shin an nada Adam A. Zango sabon sarkin Kannywood ne?

Wannan hoton dake nuna alamun cewa an nada tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango sabon sarkin masana'antar ta Kannywood ya bayyana wanda wasu dake tare da Adamun, Mansur Make-up da Maryam Gidado suka wallafa a shafukansu na sada zumunta da muhawara.


Hoton dai ya fara jawo cece-kuce yayinda masoyan Ali Nuhun suka fara mayar da raddin cewa Ali Nuhu ne kadai sarkin da suka sani domin ba'a sarki biyu a gari daya, a kwanakin bayane dai aka so a samu rashin jituwa tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango wanda kamin abin yayi kamari akamai tubka aka sasantasu, amma tun bayan wancan lokaci da alama har yanzu abubuwa basu koma daidai ba kamar da.

Bello Muhammad Bello wanda yana bangaren Adam A. Zangone dama yace za'ayi sabon zaben sarkin masana'antar a satin daya gabata inda har shima ya nuna sha'awar tsayawa takara.

Kwana biyu da suka gabata dai Adam A. Zango ya goge duk wani hoto dake dandalinshi na sasa zumuntar Instagram.

No comments:

Post a Comment