Thursday, 29 March 2018

Shugaba Buhari da mataimakinshi sun taya Bola Tinubu murnar cika shekaru 66 a Duniya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da mataimakinshi, Yemi Osinbajo da matarshi, Dolapo da gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode da sauran manyan 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnati sun halarci taron taya Bola Ahmad Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarshi da aka gudanar a otal din Eko dake jihar Legas. A wadannan hotunan sun yanka kek na musamman da akayi dan wannan rana.Tinubu dai ya cika shekaru sittin da shida a Duniya, muna tayashi murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.

No comments:

Post a Comment