Thursday, 29 March 2018

Shugaba Buhari na ziyarar aiki a jihar Legas: Ya bayar da umarnin bude duk wata hanya da aka rufe dalilin ziyarar tashi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya isa jihar Legas inda yake ziyarar aiki ta kwana biyu, a yayin ziyarar tashi ana saran zai kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar tayi dan cigaban al-umma, kamar yanda me baiwa shugaba Buharin shawara ta fannin sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ya bayyana.


A safiyar yau ne rahotanni suka rika fitowa daga jihar Legas din cewa an kulle duk wata babbar hanyar wucewar motoci a jihar, abinda ya kawo tsaikon ababen hawa da kuma tilastawa mutane tafiyar kafa.

Shugaba Buhari ya bayar da umarnin bude duk wata hanya da aka rufe a birnin Legas din dan ziyararshi, inda yace da zarar ya wuce ta hanya to a maza a bude ta dan afanin mutane.

Jihar ta Legas dai ta bayar da hutu yau Alhamis dan ziyarar ta shugaba Buhari.

No comments:

Post a Comment