Wednesday, 7 March 2018

Shugaba Buhari ya amshi ainihin kofin Duniya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amshi ainihin kofin Duniya da kasashen Duniya zasu yi gasar cinshi a kasar Rasha, yau Laraba a fadarshi dake Abuja, a zagayen da akeyi da kofin zuwa kasashe yau kofin ya iso Najeriya kuma shugaba Buharin tare da mataimakinshi, Yemi Osinbajo da ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung ne da shugaban kwamitin wasanni na majalisar kasa, Godfrey Gayya da kuma shugaban kamfanin Coca-cola yankin Afrika ta yamma Peter Njonjo ne suka kasance wajan amsar kofin.

Haka kuma shugaba Buhari ya amshi tawagar yan wasan kwallon kafa masu buga kofin gwarazan nahiyar Afrika dake cewa CHAN a fadar tashi.No comments:

Post a Comment