Monday, 5 March 2018

Shugaba Buhari ya kai ziyara jihar Taraba, Ya gana da shuwagabannin Al-Umma

A yau, Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Taraba da take fama da rikicin kabilanci, shugaba Buharin tare da gwamnan jihar, Darius Ishaku sun gana da sarakuna da kuma shuwagabannin al-ummar da rikice-rikicen suka shafa inda sukaji korafe-korafensu.Wannan ziyara dai tana zuwane bayan da shugaba Buharin ya sha suka a gurin 'yan Najeriya akan kin aki ziyarar jihohin da ke fama da rikici amma yaje daurin auren diyar gwamnan kano da gwamnan Oyo.

To amma a sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar tace shugaba Buhari ya shirya wannan ziyarane bayan da ya kammala karbar rahotanni daga jami'an tsaro da kwamitoci daya nada suyi bincike akan rikice-rikicen.


No comments:

Post a Comment