Wednesday, 14 March 2018

Shugaba Buhari ya koma Abuja daga Yobe: Zai ziyarci jihar Naija Gobe sannan kuma zai ziyarci jihar Kano ranar Juma'a

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan da ya kai ziyara jihar Yobe inda ya gana da sarakuna da kuma iyayen 'yan matan makarantar Dapchi da Boko Haram suka sace, inda yayi alkawarin ganin yayi dukkan me yiyuwa wajan dawo da 'yan matan gurin iyayensu. A gobene shugaba Buhari zaikai ziyara jihar Naija inda zai kaddamar da wani gagarumin aiki sannan kuma zai kai ziyara jihar Kano ranar Juma'a idan Allah ya kaimu.


Bashir Ahmad, me baiwa shugaban kasar shawara ta fannin sabbin kafafen sadarwane ya bayyana haka.

No comments:

Post a Comment