Saturday, 17 March 2018

Shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan Marigayi sanata Ali Wakili

A sakon da ya fitar na ta'aziyya ga iyalan Marigayi sanata Ali Wakili, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar tashi a matsayin wadda ya kadu da jinta kuma anyi babban rashi ga cigaban dimokradiyya a kasarnan, haka kuma ya bayyana marigayin da mutum me halayya ta gari da 'yan baya ya kamata suyi koyi da ita.


A sanarwar da me magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar yace, Marigayin mutum ne me dagewa wajan aikinshi da kuma yin abinda ya kamata wanda sauran ma'aikata ya kamata suyi koyi dashi.

Haka kuma yace yana mai addu'ar Allah ya jikanshi ya kuma baiwa iyalanshi, mutanen Bauchi dama 'yan Najeriya juriyar rashin da akayi.

No comments:

Post a Comment