Wednesday, 14 March 2018

Shugaba Buhari ya tabbatarwa da iyayen 'yan matan Dapchi cewa za'a dawo musu da 'ya'yansu da Boko Haram suka sace

Bayan da ya gama ganawa da sarakunan gargajiya, iyayen Al-umma a Damaturu, jihar Yobe, shugaban kasa , Muhammadu Buhari tare da  gwamna Ibrahim Gaidam sun kai ziyara makarantar 'yan mata ta garin Dapchi inda 'yan Boko Haram suka yi awan gaba da dalibai dari da goma.

Haka kuma shugaba Buhari ya gana da iyayen 'yan matan makarantar da aka sace ya kuma tabbatar musi da cewa za suyi dukkan mai yiyuwa dan ganin an dawo musu da 'ya'ya yansu da Boko Haram suka sace.

No comments:

Post a Comment