Monday, 12 March 2018

Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Benue: Zai kwashe yinin yau acan

A yaune shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Benue inda zai jajantawa mutanen jihar abinda ya farau na rikici tsakanin fulani makiyaya da manoma, kamar yanda me baiwa shugaban kasar shawara ta fannin sabbin kamafafen watsa labarai Bashir Ahmad ya bayyana, shugaba Buhari zai kwashe tsawon ranar yau a jihar ta Benue inda zai tattauna da shuwagabannin Al-umma.


A makon jiyane shugaba Buhari ya fara ziyarar jihohin da suka fuskanci rikici da aka samu salwantar rayukan al-umma, bayan da jama'ar Najeriya suka yi kushe ga shugaban kasar akan daurin auren diyar gwamnan Kano da dan gwamnan Oyo da ya halarta a Kano amma be halarci jihohin da ake rikici ba.

Amma fadar shugaban kasar ta musanta cewa wancanne dalilin ziyarar ta shugaba Buhari inda tace shugaban ya shirya ziyararce bayan da ya amshi rahotanni daga kwamitocin daya nada su je su duba yanda wadannan rikice-rikice suka faru.

No comments:

Post a Comment