Thursday, 29 March 2018

'Shugaba Buhari zai sake zuwa kasar Ingila dan duba lafiyarshi'

A wani labari da shafin Sahara Reporters suka wallafa, munji cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai sake fita kasar waje dan a duba lafiyarshi, labarin dai na cewa a satin farko na watan da zamu shiga, an shirya cewa shugaba Buharin zai kai ziyara kasar Ingila dan halartar taron kasashe renon kasar ingila amma ba'a bayyana ranar dawowarshiba.


A irin yanda ake ganin shugaba Buhari dai yana ayyukanshi kazar-kazar babu alamar rashin lafiya a tare dashi, saidai koma menene gaskiyar lamarin lokaci zai bayyana mana.

No comments:

Post a Comment