Thursday, 22 March 2018

Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Zamfara a yau

Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Zamfara a yau inda zai jajantawa 'yan jihar akan irin kashe-kashen da aka samu sanadiyyar harin 'yan ta'adda da kuma masu satar shanu da aka samu a jihar.


Jiha ta gaba da shugaba Buharin zai ziyarta itace jihar Rivers, kamar yanda me bashi shawara akan harkar sabbin kafafen sadarwa Bashir Ahmad ya bayyana.

Muna fatan Allah ya kaishi lafiya.

No comments:

Post a Comment