Monday, 5 March 2018

Shugaba Buhari zai ziyarci kasar Ghana

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar Ghana a yau Litinin dan amsa gayyatar halartar taron ranar 'yancin kasar da za'a gudanar ranar Talata idan Allah Allah ya kaimu.


A cikin wata sanarwa da me baiwa shugaban shawara akan harkar watsa labarai, Femi Adesina ya fitar, ya bayyana cewa shugaba Buharine kadai shugaban kasar waje da kasar Ghanar ta gayyata a matsayin baki na musamman kuma wanda zai gabatar da jawabi a ranar.

Muna fatan Allah ya kaishi ya kuma dawo dashi gida lafiya

No comments:

Post a Comment