Saturday, 17 March 2018

Shugaba Buharine waliyyin Fatima Dangote: Sadakinta Dubu 500

A jiyane aka daura auren diyar attajirin dan kasuwa, Fatima Aliko Dangote da dan gidan tsohon shugaban 'yan sanda, Jamil M.D Abubakar a jihar Kano, shugaban kasa Muhammadu Buharine ya zama waliyyin amarya inda ya bayar da aurenta ga wakilin ango akan sadaki naira dubu dari biyar.


Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ne ya daura auren sai kuma limamin Kano yayi addu'a,  kamar yanda Daily Trust ta ruwaito, manyan baki da suka hada da Bukola Saraki, Yakubu Dogara da Gwamnoni da sauran manyan 'yan siyasa da masu kudi, kai hadda me kudin Duniya, Bill Gates ya halarci daurin auren.

Muna fatan Allah yasanya Alheri.

No comments:

Post a Comment