Wednesday, 28 March 2018

Shugaban kasar Korea ta Arewa ya ziyarci kasar waje a karin farko shekaru 7 bayan hawa karagar mulki

Shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong Un yayi ziyara ta farko shekaru bakwai tun bayan da ya dare bisa karagar mulkin kasar, Kim ya gana da takwaranshi na kasar China, Xi Jinping a karon farko a hukumance cikin shekaru bakwai.


Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa shugaban kasar China' Xi ya bashi labarin tattaunawar da sukayi da Kim din kuma sun tattauna batutuwan cigaba inda har Kim din ya bayyana sha'awar tattaunawa da Trump.

Saidai Trump din ya bayyana cewa duk da haka takunkumi da kuma matsin lambar da sukewa kasar ta Korea ta Arewa ba zai canjaba.
Aljazeera/ Time.

No comments:

Post a Comment