Tuesday, 6 March 2018

Shugaban kasar Liberia ya roki shugaba Buhari ya taimakamai da malaman karanta 6000

Shugaban kasar Liberia, George Weah ya roki Shugaba Buhari ya taimakawa kasarshi da malaman makaranta guda dubu shida, a ziyarar da ya kawo Najeriya jiya, Litinin, Weah yace kasarshi na fama da matsalar karayar tattalin arziki domin kayan albarkatun kasa da kasar ke fitarwa kasuwanin Duniya dan samun kudin shiga, dajarsu ta karye.


Ya kara da cewa mutanen kasar sun zabeshi dan ya kawo musu canji akan irin rayuwar da suke yi a baya kuma Najeriya ce kasar da ta taimakawa Liberiar lokacin da take cikin yakin basasa kuma har ta horar da sojojinta wadanda yanzu suma suna bayar da taimako wajan kawo zaman lafiya a kasashen waje.

Weah yace wannan yasa ya garzayo gurin shugaba Buhari akan shawara da taimako akan yanda zai farfado da tattalin arzikin kasarshi.

Ya kuma yi rokon masu zuba jari da su je kasar tashi zasu sameta guri me yanayi me kyau ma gudanar da kasuwancinsu.

No comments:

Post a Comment