Thursday, 22 March 2018

Shugaban kasar Myanmar/Burma yayi murabus dan hutawa rayuwarshi

A jiyane shugaban kasar Myanmar, Htin Kyaw yayi murabus daga kan kujerar mulkinshi inda ya bayyana cewa yana so yaje ya huta, dama dai akwai rade-radin cewa shugaban kasar me shekaru saba'in da daya bashi da lafiya da aka rikayi a kwanakin baya wanda fadar shugaban ta karyata. Da dama suna bayyana shugaban kasar a matsayin hoto domin kusan ana ganin firaiministar kasar Aung San Su Kyi ce take yin kusan komai na harkar gwamnati.


Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa nan bada dadewa ba majalisar kasar zata sake nada wani sabon shugaban, ana sa ran Su Kyi ce zata zama shugabar kasar ganin cewa yawancin 'yan majalisar kasar suna tare da ita.

A kasar ta Myanmar/Burma ce aka samu jami'an soji da yiwa musulmai tsiraru 'yan kabilar Rohingya kisan kare dangi wanda yayi sanadiyyar kwarar 'yan gudun hijira zuwa kasashe daban-daban, yawancin a kafa. Sojojin dai sun kare kansu da cewa suna fada da 'yan kabilar ta Rohingyane dake adawa da gwamnati da kuma kashe jami'an tsaro.

Duniya gaba da ya da kuma kungiyoyin kare hakkin bul-adama sunyi Allah wadai da wacan Lamari.
CNN/Guardian.

No comments:

Post a Comment