Thursday, 1 March 2018

Shugaban sojin sama ya koma Maiduguri da zama dan ganin an dawo da 'yan matan Dapchi gida

Da alama gwamnatun tarayya ta mayar da hankali sosai wajan ganin an gano inda 'yan matan makarantar Dapchi suke da mayakan Boko Haram suka sace, Shugaban hukumar sojan sama, Air Marshal  Sadik Abubakar ya koma Maiduguri da zama dan kula da irin yanda neman 'yan matan yake gudana da kanshi.


Me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Muhammad Munguno tare da shugaban sojojin saman sun kaiwa gwamnan jihar Yobe ziyara inda suka tattauna muhimman batutuwa akan ceto 'yan matan.

Muna fatan Allah ya bayyana su.

No comments:

Post a Comment