Tuesday, 13 March 2018

Shugaban 'yan sanda ya bijirewa umarnin shugaba Buhari

A ziyarar da ya kai jihar Benue, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana mamakinshi da jin cewa shugaban 'yan sanda Ibrahim Idris ya bar jihar ta Benue zuwa jihar Nasarawa bayan da shugaban kasar ya bashi umarnin komawa jihar ta Benue da zama dan tabbatar da kawo karshen rikice-rikicen dake faruwa a jihar dake sanadiyyar salwantar rayuka.


Duk da yake cewa shugaban 'yan sandan ya bi umarnin shugaban kasar na komawa jihar ta Benue amma daga baya sai ya bar jihar zuwa jihar Nasarawa, shugaba Buhari ya bayyana hakane a cikin jawabin da yayi a jihar ta Benue bayan da gwamnan jihar ya bayyanawa Buharin cewa shugaban 'yan sandan ya nuna son rai wajan  daukar matakin da ya dace akan rikicin.

Shugaba Buharin dai yace idan ya koma Abuja zai kira shugaban 'yan sandan dan yaji dalilin shi na yin hakan kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment