Monday, 5 March 2018

Shugabannin matan jam'iyyar APC na jihohi sun kaiwa A'isha Buhari ziyara

Shugabannin matan jam'iyyar APC na jihohi talatin da shida dake kasarnan sun kaiwa, matar shugaban kasa, Hajiya, A'isha Buhari ziyara, A'isha ta gana dasu inda ta bayyana cewa sun tattauna akan harkokin da suka shafi mata kuma taji dadin ziyarar tasu.A jawabin da tayi lokacin ganawar da matan APC din ta yaba musu akan kokarin da sukayi na hadin kai har suka hada kungiya, sannan tayi kira ga mata da su shiga harkokin gwamnati a rika damawa dasu. Ta kara da cewa koda shirin ta na gidauniyar ta da take tallafawa matasa da mata da ita ta Future Assured tsarine na kara yada muradun jam'iyyar APC.

Ta bukaci matan suma da su yi kokari wajan kara yada kyawawan muradun jam'iyyar a tsakanin mutane.


No comments:

Post a Comment