Wednesday, 7 March 2018

T. Y Shaban ya caccaki Nura Hussain akan wai beyi magana akan abinda diyar Ganduje tayi ba amma lokacin Rahama Sadau yana gaba-gaba akan kiran a hukuntata

Bayan da hotunan diyar gwamnan jihar Kano da akawa aure kwanannan, Fatima Abdullahi Umar Ganduje da dan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajomobi suka bayyana yana sumbatarta, tauraron fina-finan Hausa, T. Y Shaban ya fito ya bayyana ra'ayinshi akai inda yace da dan fim ne yayi wannan abu da kaji dirar ayoyi, to a wancan lokacin be bayyana da wa yake ba amma yanzu kam ya fito ya nunawa daya daga cikin masu fada aji a masana'antar ta fim din Hausa yatsa.


A wani rubutu da Shaban din yayi ya caccaki Nura Hussain akan cewa lokacin da Rahama Sadau tayi bidiyon waka da mawqki Classiq yana daya daga cikin wadanda suka fara kiraye-kirayen a hukuntata amma yanzu ga diyar Gwamna Ganduje tayi hotunan da basu dace ba amma beyi magana ba.

Gadai abinda T. Y Shaban din ya bayyana kamar haka:

"Mallam Nura Hussain Na daya daga cikin masu fada aji a masana'antar shirya Fina finai ta kannywood. Mallam Nura ya taka rawar gani lokacin da jaruma rahama sadau ta fito a wani video Waka Wanda takai har Saida hadaddiyar kungiyar masu shirya Fina finai (moppan)suka dauki matakin ladabtarwa a kanta. TAMBAYA: shin Mallam Nura ba muji yayi wani sharhi akan pre wedding picture Na Fatima GANDUJE da Idris AJIMOBI ba Wanda duniya ta gani karara yana shamata Baki kuma hannuwansa akan nononta? Shin ko fadakarwar an kebe tane akan wasu gungun mutane ne?"

Saidai mutane da dama da suka yi sharhi akan wannan magana ta T. Y Shaban basu goyi bayanshi ba, da yawa cewa sukayi ai Nura Hussain a masana'antar fim din Hausa yake da karfim fada aji amma magana akan abinda diyar gwamna tayi ba huruminshi bane.

Ga abinda wasu ke cewa akan wannan batu.


No comments:

Post a Comment