Sunday, 11 March 2018

T. Y Shaban ya cire caccakar da yayiwa Nura Hussain daga shafinshi

Tauraron fina-finan Hausa, T. Y Shaban ya cire caccakar da ya yiwa abokin aikinshi, Nura Hussain akan kin yin magana dangane da hotunan bikin diyar gwamnan Kano daya zarge da kinyi amma lokacin Rahama Sadau tayi bidiyo da Classiq yana gaba-gaba wajan kiran a hukuntata.


Wannan batu da Shaban ya dauko ya dauki hankulan mutane sosai inda akaita bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai kuma da yawa basu goyi bayanshiba, amma daga baya Shaban ya fito yace ba sukar Nura yake yi ba kawaidai ya kawo batunne dan misali dashi, daga bayama sai ya goge maganar da yayi akan Nuran daga dandalinshi na sada zumunta.

No comments:

Post a Comment