Thursday, 8 March 2018

T. Y Shaban yayi amai ya lashe akan caccakar da ya yiwa Nura Hussain akan hotunan diyar Ganduje

Bayan da tauraron fina-finan Hausa, T. Y Shaban ya caccaki abokin aikinshi, Nura Hussain da cewa me yasa beyi magana akan hotunan da diyar gwamnan Kano, Fatima Ganduje ta dauka da mijinta ba, mutane da dama da sukayi sharhi akan wannan batun basu goyi bayanshi ba inda suka cemai ba hurumin Nura bane yayi magana akan diyar gwamnan, kuma abinda Rahama Sadau tayi da wanda diyar gwamnan tayi ba hanyarsu daya ba.


T. Y din ya fito yace bawai yana danganta Nura Hussain da maganar doyar gwamna bane, kawai dai ya kawo labarinne dan yayi misali dashi akan abinda ya faru da diyar gwamnan.

Ga abinda ya fada kamar haka:

"Ba Ina nufin alakanta Brother Mallam Nura Hussain bane da hoton bikin Fatima GANDUJE da Idris AJIMOBI, illa rawar da malamin ya taka a matsayinsa Na jarumi wurin tsawatarwa Rahama sadau akan fimdin da tayi...da kuma ladabtar da ita a part 1. To, shine al'umma take kallo yana faruwa a yanzu kuma sunan malamin ya zama Matashiya abin kwatance a part 2 yanzu. kukan kucciya ne kawaii mukeyi."

Wanan batu dai ya dauki hankula sosai.

No comments:

Post a Comment