Tuesday, 27 March 2018

'Tabbas an kawo mana korafin cin zarafin da wasu sojoji su kawa mutane'>>Ministan tsaro

A makon jiyane, tsohon ministan tsaro T.Y Danjuma yayi zargin cewa jami'an tsaron kasarnan na goyawa Fulani makiyaya baya a kisan da sukewa mutane a kasarnan, musamman a jiharshi ta Taraba, inda ya bukaci 'yan Najeriya da su fito su kare kansu, a wata hira da yayi da jaridar Punch, ministan tsaro Mansur Dan Ali ya shaida cewa akwai jami'an soji da aka kawo musu korafi a kansu.


Ya kuma kara da cewa sun dauki matakin da ya dace akansu. Saidai ya kara da cewa basu samu irin wannan korafi daga jihar Taraba ba.

Yayi kira ga mutane da idan wani jami'in tsaro yaci zarafinsu da su fito su bayyanawa ma'aikatar tsaro ta kasa ko kuma ma suje duk wata hukumar soji dake kusa dasu su kai kara za'a dauki matakin daya dace. Kada su ji tsoro.

Yace ba zasu iya daukar mataki akan korafin da akayi na gama gariba saidai wanda aka bayyana ainihin wada suka aikata laifin

No comments:

Post a Comment