Tuesday, 27 March 2018

Tinubu be halarci taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC ba

A daren jiyane jam'iyyar APC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja wanda shugaba Buharin ya jagoranta, saidai wani abu daya dauki hankulan mutane akan wannan taro shine rashin ganin daya daga cikin jigon jam'iyyar, Bola Ahmad Tinubu a gurin taron.


A taron jam'iyyar na kwanakin baya da aka gudanar, an bayyana cewa za'a tsawaita lokacin rikon mukaman shuwagabannin jam'iyyar abinda Tinubun ya kalubalanta amma sauran 'yan jam'iyyar basu goyi banayanshi ba.

Haka kuma shugaba Buhari ya nada Tinubu ya jagoranci daidaita wadanda ke rikici a jam'iyyar ta APC amma rahotanni sun nuna cewa Tinubun be nada koda mutum guda ba da zasuyi aikin tare ba, shugaba Buhari, mataimakinshi da shuwagabannin majalisun kasarnan da shugaban jam'iyyar ta APC da gwamnonin jam'iyyar sun halarci taron, kamar yanda jaridar Vanguard ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment