Tuesday, 13 March 2018

Trump ya sallami sakataren harkokin wajen Amurka Tillerson kwana daya bayan da ya ziyarci Najeriya

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori Sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson daga kan mukaminsa, sannan ya maye gurbinsa da wani jami'in hukumar leken asirin kasar, CIA Mike Pompeo. Mr Trump ya bayyana korar ce a shafinta na Twitter, yana mai gode masa bisa aikin da ya yi wa kasar.


Ya kara da cewa sabon sakataren wajen na Amurka zai yi "kyakkyawan aiki".
An nada Mr Tillerson, wanda tsohon shugaban kamfanin ExxonMobil ne, kan mukamin shekara daya da ta wuce.

Shugaban na Amurka ya kuma nada Gina Haspel domin zama mace ta farko da za ta shugabanci CIA.

Rahotanni sun sha nuna yadda ake rashin jituwa tsakanin Mr Trump da Mr Tillerson, musamman kan yadda suke bayyana da mabambantan manufofi kan manufofin harkokin wajen kasar - kama daga batu kan Korea ta Arewa zuwa Iran.

Ranar Litinin tsohon sakataren harkokin wajen na Amurka ya kai ziyara Najeriya kuma lokacin da ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari, ya jaddada aniyar kasarsa wurin taimakwa Najeriya kan yaki da ta'addanci.
bbchausa.


No comments:

Post a Comment