Friday, 9 March 2018

Tsakanin Marigayi Sheik Mahmud Gumi Da Wani Maroki

Wata rana wani maroki mai hikima ya je gidan marigayi Shiekh Dr. Muhammad Gumi dake garin Kaduna domin ya gana da shi.Lokacin da ya je gidan misalin karfe 11 na rana sai ya tarar da Malam na bacci. Bayan ya yi sallama, almajiran Malam suka amsa sai ya bukaci da a yi masa sallama da Malam. Aka nunawa wannan Bawan Allah, a irin yanzu malam ba ya ganin wani sai lokacin Sallar Azahar zai fito, ya jira har zuwa lokacin sallar ta Azahar.

Wannan mutum ya yi ta musu magiya akan Su taimaka masa su Sallamo masa Malam. Amma Sam Almajiran suka ce Ba'a ganin a irin wannan lokaci. Lokacin da wannan bawan Allah ya tabbatar bazasu Kira masa Malam Ba sai yace, "Ai kuwa yanzu Zai fito".

Sai wannan mutumin ya je daidai kofar taka (Window) din Malam, sai ya fara kiran Sallah, Allaahu Akbar! Allaahu Akbar!! Ya dai raira kiran sallah har zuwa karshe. 

Nan take Malam Gumi ya fito ya tambaya garin yaya na ji an yi kiran Sallah alhali lokaci bai yi ba. Sai aka nunawa Malam wannan Bawan Allah.

Sai wannan mutumin ya ce, "Ni na kira Sallah, saboda an ce wai ba za ka fito yanzu ba, sai lokacin sallar azahar, shi ya sa na kira sallar.

Malam ya yi murmushi ya ce, "To naji me ke tafe da kai?" Wannan bawan Allah ya ce, "Na zo ne yin maula Allah shi gafarta Malam." Malam yace, "Yanzu abin ya kai har Malamai ake yi wa Dan Kwairo (Maula)?".
Sai wannan bawan Allah yace, "Ai su ya fi dacewa saboda su suka karanta ayar da ta hana yin bara, kuma su suka san falalar yin sadaka." Nan malam ya yi murmushi ya shiga cikin gida ya samo aron kudi ya ba shi.

Saboda a lokacin an ce Malam ba shi da ma kudi sai da ya aro wajen Iyalinsa. Allahu Akbar. Allah ya jikan Malam Ya gafarta masa.
rariya.

No comments:

Post a Comment