Thursday, 8 March 2018

Uwargidan shugaban kasa, A'isha Buhari ta nuna takaici bisa cin zarafin yara mata

Da take jawabi a gurin taron ranar mata ta Duniya a Abuja, uwargidan shugaban kasa, Hajiya, A'isha Buhari tayi kira ga masu sacewa da kuma musgunawa yara mata da cewa su bar musu 'ya'yansu, uwargidan shugaban kasar ta bayyana takaici akan irin cin zarafin da akewa yara mata.Tace musamman satar 'yan matan makaranatar Chibok da na Dapchi abin tashi hankaline kuma tana fatan kokarin da gwamnati take yayi sanadin dawo da 'yan matan gurin dangi da Iyayensu.

Uwargidan shugaban kasar tayi kira ga matan gwamnoni da suka halarci taron dasu je jihohinsu su yada wannan sako nata na cewa a bar musu yaransu hakanan domin ya shiga sako da lungu na kasarnan.

No comments:

Post a Comment