Monday, 19 March 2018

Vladimir Putin ya lashe zaben shugaban kasar Rasha karo na 4

Vladimir Putin, President of Russia speaks during the Preliminary Draw of the 2018 FIFA World Cup in Russia at The Konstantin Palace on July 25, 2015
Vladimir Putin zai cigaba da mulkin Rasha na wasu shekaru shida baya da ya lashe zaben shugaban kasa a karo na hudu.Bayan da aka kusan kammala kididigan kuri'un da aka kada, ya sami kashi 76 cikin dari, inji hukumar zabe ta kasar.


An hana babban mai adawa da Mista Putin, Alexei Navalny daga tsayawa takara a wannan zaben.
Bayan da aka bayyana wani bangare daga cikin sakamakon zaben, ya gaya wa magoya bayansa cewa masu kada kuri'a "sun fahimci tasirin cigaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan".
Ya fada wa manema labarai cewa ba zai cigaba da neman shugabancin kaar ba har illa ma sha Allah:
"Wannan abin dariya ne. Kana ganin zan cigaba da zama a nan har sai na kai shakara 100 da haihuwa? Ina!" inji shi.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment