Thursday, 22 March 2018

Wani Babban Mawakin Kasar Jamus Zai Buga Casun Farko A Kasar Saudiyya

Saudi Arabiya ta shirya kidan 'Party' na D.J na farko a kasar a yunkurin ta na kawo sauyi cikin al’adun kasar. Shafin yanar gizo na Arabian business ya rawaito cewa, Saudi Arabiya ta bada sanarwar shirin gayyato shahararren DJ a duniya, Armin Van Buuren, zuwa bikin rawa na farko a masarautar.


Za a yi bikin ne a katafaren Birnin Tattalin Arziki na Sarki Abdullah, a ranar 17 ga watan Yuni, haka kuma a wurin bikin ne Saudiya zata bayyana shirin ta na kashe makudan biliyoyin kudi wajen gina wuraren wasa da za’a rika gayyato Fasihan kasashen yamma karkashin sabon shirin sauya harkokin nishadi a kasar.

Makadin zamanin wato dj, dan kasar Jamus shine na farko a duniya kamar yadda mujallar DJ Mag ta bayyana sau biyar a jere a Amurka da fadin duniya, shi ke rike da kambun wanda ya fi kowanne DJ shiga jerin gwanayen kidan zamanni na Electric da Rawa na Muajllar Billboard har sau 21.

Ma’aikatar Nishadi ta Saudiya ita ta dauki nauyin shirin wanda kamfanin Brackets ya shirya.
Wadannan sauye-sauye sun biyo bayan shirin Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ko MBS, na “Vision 2030” da nufin kawo sauyi a zamantakewa ciki har da bai wa mata damar tuka mota da halartar wasannin kwallon kafa a kasar ta Saudiyya.

Zamanantar da kasar mai ra’ayin mazan jiya, na daga cikin sauye-sauyen da ya ke kokarin yi da kuma kirkiro sabbin hanyoyi masu dorewa domin inganta tattalin arzikin kasar.
Rariya

No comments:

Post a Comment