Thursday, 1 March 2018

Wani bincike ya bayyana cewa amfanin da Asuwaki wajan wanke baki yafi amfani da Burosh da Makilin gayara hakora

Wani bincike da kwararru sukayi akan wasu itacen da ake asuwaki dasu ya bayyana cewa amfani da asuwakin wajan wanke baki yafi amfani da burushin zamani da makilin da akeyi wajan gyaran hakora da hana lalacewarsu.


Kamar yanda jaridar Guardian ta ruwaito, binciken da kwararru a jami'ar Olabisi Onabanjo dake jihar Ogun suka yi kuma wanda aka wallafashi a mujallar kasar ingila dake wallafa bincike akan kiwan lafiya ya kara da cewa asuwakin yana kara karfin maza da taimakawa wajan haihuwa da sauran wasu magunguna a jikin mutum.

No comments:

Post a Comment