Sunday, 25 March 2018

Wani mara lafiya yayi firgigit daga gadon asibiti ya bi budurwarshi da gudu saboda ta dauki wayarshi

Wani mutum dake jiyya a gadon Asibiti na Kansas dake kasar Amurka yayi firgigit yabi budurwarshi da gudu yayin da ta dauki wayarshi, mutumin ya fito daga dakin da aka kwantar dashi da gudu yana tambayar ma'aikatan asibitin basu ga wata da wayarshi ba?.


Nan dai ya nufi gurin da ake ajiye motoci, ai kuwa yayi sa'a ya ga motarta bata tafi ba haka ya bita hadda hawa bayan mota yana fadin ta bashi wayarshi ita kuwa ta tayar da motarta ta tsere.

Yana yin abin da kuma yanda ya bayar da mamaki yasa wani ya dauki mutumin hoton bidiyo


Dailymail/UK

No comments:

Post a Comment