Tuesday, 6 March 2018

Wata 'yar jarida ta soki fim din Rariya da cewa zai iya sa iyaye su dena aika 'ya'yansu mata makarantun jami'a: Rahama Sadau ta mayar da martani

Yar jarida kuma tsohuwar ma'aikaciyar BBC, Kadaria Ahmed ta soki fim din da tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta shirya me suna Rariya, Kadaria ta bayyana cewa a jiya ta dan kalli wani sashe na fim din Rariya na tsawon mintuna ashirin kuma abinda ta fahimta shine, shirin fim din zai iya sa iyaye su dema aika 'ya'ya mata makarantun jami'a.Kadaria ta kare zancenta da tambayar Rahama Sadau cewa, amma na tabbata ke ba abinda kike burin cimmawa kenan ba a wannan fim din.

Rahamar ta amsa da cewa, fatana shine shirin fim din Rariya ya sa iyaye su kara saka ido akan 'ya'yansu su kuma nuna musu sanin mutuncin kansu da darajar karatunsu fiye da rudin da wasu mutane ke musu da kayan alatu na karya. A karshe ta cewa kadaria da kin kalli fim din har zuwa karshe da yafi.

No comments:

Post a Comment