Sunday, 25 March 2018

Watakila Pogba ya bar Manchester United

Manchester United tana shirin sayar da Paul Pogba dan kwallon tawagar Faransa da ta saya mafi tsada a tarihi. United za ta yi amfani da kudin da ta sayar da Pogba, domin taya wasu 'yan kwallon da ta ke son yin zawarci a badi.


Jaridar Mirror ta ce United din za ta yi zawarcin Raphael Varane mai tsaron bayan Real Madrid da Toni Kross dan kwallon tawagar Jamus.

Haka kuma jaridar ta ce United din za ta tuntubi mai tsaron bayan Paris St-Germain, Marquinho da Marco Verratti dan kwallon tawagar Italiya da kuma Alex Sandro mai tsaron bayan Juventus.

United tana ta biyu a kan teburin Premier, za kuma ta buga wasan daf da karshe da Tottenham a Gasar Cin Kofin FA a cikin watan Afirilu a Wembley.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment