Friday, 2 March 2018

Ya Dace Nijeriya Ta Yi Koyi Da Saudiyya Wajen Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Masu Safarar Miyagun Kwayoyi, Inji She

An bukaci Gwamnatin tarayyar Nijeriya da ta yi koyi da kasar Saudiyya wajen zartar da hukuncin kisa akan dillalan muggan kwayoyi, duba da yadda suke haifar da munanan matsaloli wajen bata kwakwalwa da tunanin matasan kasar nan. 


Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa Ikamatus Sunnah na Kasa Al Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya yi wannan kiran, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a gidan shi dake garin Kaduna. 

Sheikh Bala Lau yace kiran ya zamo wajibi ne bisa la'akari da yadda dillalan miyagun Kwayoyi ke taka muguwar rawa wajen jefa rayuwar Matasan kasar nan cikin hatsari, sannan idan muka lura da kyau shaye shayen muggan Kwayoyi na kashe cigaban Matasan ne ya mayar dasu koma baya, wannan dalilin ne ya sanya kasar Saudiyya daukar matakin kashe duk wanda keda burin kashe tunanin Matasan kasar ta, wato kafin ka kashe mana Matasan mu bari mu dauki matakin kawar da kai, wannan ya taimaka sosai a kasar Saudiyya wajen samar da Al'umma ta gari, kuma tabbas idan Nijeriya ta dauki matakin yin haka shakka babu kwalliya za ta biya kudin Sabulu. 

Malamin wanda ya koka matuka akan yadda shaye shaye ke neman zama ruwan dare a Nijeriya musanman yankin Arewacin kasar, inda a yanzu ake samun Matan Aure da 'Yan Mata gami da Zawarawa sun tsunduma harkar shaye shaye, bangaren Matasa kuwa wannan ba'a magana shaye shaye ya zama wata alama da suke kallo ta wayewa a wajen su, karin abin damuwa da takaici a yanzu shine yadda ake samun hatta wasu Malamai suma sun tsunduma harkar shaye shaye, ashe wannan wani lamari ne wanda bai kamata Gwamnati ta yi wasa dashi ba. 

Imam Abdullahi Bala Lau ya kuma bayyana kokarin da Kungiyar Izala keyi na ganin an samu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin  Al 'ummar Musulmin Nahiyar Afirka gaba daya, wanda wannan na daga cikin dalilan da ya sanya Kungiyoyin Musulmi dake nahiyar Turai suka gayyace su kwanakin baya domin yaba musu akan kokarin da sukeyi na ciyar da Musulunci gaba, kuma hakika ziyarar da su ka kai a kasashen Turai din, sun gano babu Addinin da ake tururuwa wajen shigar shi yanzu a Duniya kamar Addinin Musulunci, kuma Musulmin wadannan kasashe sun nuna matukar gamsuwa da ayyukan Izala, wannan ne ya sanya nan da makwanni biyu masu zuwa, za su kara halartar Kasashen Amurka da Canada bisa ga gayyatar Musulman wadannan Kasashe domin cigaba da yada kalmar Allah. 

Shugaban Kungiyar na Izala ya cigaba da cewar, kamar yadda aka sani Kungiyar Izala wacce ta lashe shekaru 40 tana da'awa akan Sunnah da yakar Bidi'o'i da miyagun Al'adu, hakanan Kungiyar ta tsaya tsayin daka wajen dora jama'a musanman Matasa akan karantarwa Kitabu da Sunnah, da kokarin fahimtar da su hakikanin karantarwa Musulunci, domin kamar yadda ya bayyana rashin samun sahihin ilimin Musulunci ne ya kawo mana shigowar wasu bakin akidu kamar su Khawarij wadanda sune sila na shigowar Boko Haram kasar nan.
rariya.

No comments:

Post a Comment