Monday, 26 March 2018

Yadda Aka Ciri Sama Da Bilyan 100 Daga Bankin Nijeriya Aka Kai Gidan Jonathan

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa tana da Cikakkun shaida kan yadda tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya bayar da umarnin cire sama da Bilyan 100 aka kai masa gida don rabawa 'yan siyasa a makonni biyu kafin  zaben 2015.


Tun da farko ne dai, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ya nuna cewa wadannan kudade da aka zare daga Babban Bankin Nijeriya ya yi matukar girgiza tattalin arzikin Nijeriya inda ya nuna cewa har yanzu ana fuskantar tasirin cire wadannan kudaden.
rariya

No comments:

Post a Comment