Wednesday, 14 March 2018

Yakubu Dogara ya wa Abdulmumini Jibril barka da dawowa Majalisa

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara kenan a lokacin da yake wa dan majalisa me wakiltar kiru da bebeji, Abdulmumini Jibril barka da dawowa majalisar bayan kwashe kusan shekara guda da dakatar dashi da akayi daga majalisar.


A jiyane, Yakubu Dogara ya bayyana cewa majalisar ta dagewa Abdulmumini Jibril dakatarwar da ta yi mishi bayan da ya rubuta takardar bayar da hakuri da kuma cika wasu sharuddan da aka gindaya mishi.

No comments:

Post a Comment