Friday, 9 March 2018

'Yan Buhariyya dake zagina akan na soki gwamnatin Buhari ku kiyayeni: Kunsan duk lokacin da nayi magana sai ta girgiza kasarnan'>>Ummi Zeezee

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta mayar da raddi akan masu zaginta saboda ta soki shugaba Buhari tace su kiyayeta, sun santa sarai, ba ta da tsoro kuma sun san cewa a koda yaushe idan tayi magana akan jam'iyyar APC sai ta girgiza kasar, Ummin dai ta saka wannan hoton na sama inda wani yake yabon irin sukar da ita da Fati Muhammad suke wa shugaba Buhari.


Ga abinda tace kamar haka:

"DEAR BUHARIYYAS ,zan baku amsa akan karuwai da kuke Kiran mu dashi dan mun fadi gaskiya. nan ba da dadewa ba ku saurareni dan kun sanni sarai kamar yunwan cikinku.duk yawanku bana tsoron fiskantarku wanjen yi muku RADDI domin ni a rayuwata ban San wani abu da ake kira tsoro ba balle tsoron wani kato ya takamin birki wajen fadan gaskiya akan ra,ayina dan gane da harkar siyasa.ni Allah kadai shi nake tsoro ba mutum mai rauni irina ba....kuma kunsan ni inna tashi maganah akan apc maganah daya nakeyi Wanda take girgiza kasar gaba daya,ko kun manta maganar danayi last month akan shugabancin apc Wanda maganar ta tashi hankalin manyan mutane na apc? dan haka ku dinga shiga taitayinku dani"

No comments:

Post a Comment