Thursday, 15 March 2018

'Yan kasar waje maza na auren karya a Najeriya dan samun saukin yin ayyuka

Shugaban hukumar shige da fice ta kasa, Muhammad Babandede ya bayyanawa manema labarai cewa sun gane yanda wasu 'yan kasashen waje suke yin auren karya da wasu matan Najeriya, yace, 'yan kasashen wajen suna yin hakane dan gujewa kudin zama da ya kamata ace wanda ba dan kasa ba ya bayar da kuma samun yin ayyuka cikin sauki.


Babandede ya kara da cewa wasu 'yan kasar wajen ma sunzo yawan shakatawane kawai sai amma dan kar su biya kudin zaman da zasu yi sai su yi auren karya wanda cikin kankanin lokaci sai kuma su fice daga kasar, ya bayyana cewa yanzu haka sun kama wasu masu irin wannan dabi'a, kuma zasu saka ido sosai akan baki 'yan kasar waje masu shigowa kasarnan.

Ya kuma ce zasu hana baiwa wani dan kasar waje aikin da 'yan Najeriya zasu iyayi duk dan kokarin magance irin wadancan matsalolin. Inda yace daga yanzu duk wanda zau ba takardar shedar zama a Najeriya sai yayi wata shidda tukuna dan kar ya yiwa doka alaye

No comments:

Post a Comment