Friday, 2 March 2018

'Yan matan Dapchi na tare da dana da bokanshi cikin koshin lafiya>>inji mama Boko Haram

Hajiya Aisha Wakil wacce aka fi sani da “Maman Boko Haram”, ta ce 'yan Boko Haram din da suka sace 'yan matan Chibok sun tuntube ta. A wata hira da kamfanin dillacin labarai, NAN, Aisha Wakil ta ce bangaren Abu Mus’ab Albarnawi sun tuntube ta kuma sun bayyana mata cewa yan matan na hannunsu. 


Tace: “Sune suka kira ni, kuma sun bayyana mini cewa sun ji abinda kuka fada kuma sun ce za su saki 'yan matan. 

“Na roke su cewa kada wannan ya zama wani kwanaki 1000 na 'yan matan Chibok, sai suka yi murmushi suka ce a’a.” 

“Na tambaye su inda zan iya zuwa domin ganawa da 'yan matan cikin kwanaki biyu, amma ba su ce komai ba.” 

“Ina tabbatarwa 'yan Nijeriya cewa suna tare da yarona Habib da abokansa; Habib yaro ne mai kirki, ba za su taba su ba, kuma ba za su kashe su ba.”

 “Zai saurare mu, kuma ya nuna cewa yana son zaman lafiya. Ko shakka babu za su ba mu 'yan matan. Ina kira ga 'yan Nijeriya da su kwantar da hankulan kuma mu ci gaba da addu’a.”

Ta yi wannan magana ne bayan gwamnatin tarayya ta ce suna neman 'yan matan a wasu kasashen da ke makwabtaka da Nijeriya.
rariya.

No comments:

Post a Comment