Friday, 30 March 2018

'Yanda naga yaki da idona: Allah ya taimakeni nasha da kyar'>>Mansura Isa

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana yanda taga irin yanda ake rigimar siyasa da idonta jiya a garin Kaduna, kuma Allah ya taimesu suka sha da kyar, Mansurah tace bata taba ganin yaki da idon taba sai jiyan, da suka zo wucewa ta Kawo, Kaduna inda matasa suka rika rigima akan zaben fidda gwani na 'yan takarar kansila da akayi a jiyan.


Mansurar dai tayi kira ga matasa akan cewa shi wanda suke wannan tashin hankali akanshi da 'ya'yanshi basa gurin amma su gasu zasu illata kansu, a karshe dai tayi fatan Allah ya shiryesu.

Ga abinda tace kamar haka:

"Alhamdulillah we were saved today along kawo kaduna state. No any politician worth dying for. Wallahi mu lura mu kare kanmu da kasar mu. Ban taba ganin yaki ido da ido ba sai yau. Kuna nan kuna kashe kanku while shi da kukeyi a kansa yabar garin ko kasa da iyalin sa. Yaushe zamuyi hankali? Yaushe zamu gane cewa lafiyar mu da lafiyar kasa itace ta farko kafin wani abu. Kuna ta yanke yanke, kuna jiwa junan ku ciwo, kuna kashe junan ku da sunan siyasa ba Dan Addini ko DAN Allah da Manzon saba. Mai zasu baku? In kunji ciwo ko asibiti bazaku ga wani Dan siyasa yazo duba kuba. Duk alkawarin da zasu muku wallahi wallahi duk karya ne. 
Allah ya shirya
Allah yasa ku gane
Allah ya gyara mana kasar mu
Allah yasa mu gama da duniya lafia ameen."

No comments:

Post a Comment