Wednesday, 14 March 2018

'Yawun mace na kara kaifin hadda'

Wani Malamin addinin Musulunci ya bayyana cewa miyaun bakin mace yana da matukar amfani musamman ga masu kokarin hadda. Sheikh Ahmad Tijjanu Yusuf Guruntum wanda babban Shehin Malamin addinin Musuluni ne a Garin Bauchi a wani karatu da yayi ya bayyana cewa miyaun mace yana da amfani kwarai domin yana kara kaifin harda sosai.


A addinin Musulunci ma dai sumbantar iyali abu ne mai kyau inda wannan malamin ya bayyana wani babban fa’idar da ‘daliban ilmi ba su san shi ba. Malamin ya kafa hujja da wani hadisin Annabi a littafin Sahihul Bukhari.

Dama dai masana a kimiyya tuni sun ce sumbanta a baki yana taimakawa wajen maganin ciwon kai da rage ciwon hawan jini, haka kuma ana so mata masu al’ada su rika yawan sumbanta domin rage radadin al’adar.

Naija.

No comments:

Post a Comment