Saturday, 10 March 2018

Za'a fara koyar da darussan kimiyya cikin harsunan gida

Gwamnatin Najeriya ta ce tana gaf da fara aiwatar da shirinta na fara koyar da lissafi da sauran darussan kimiyya cikin harsunan gida a makarantun Firamare da Sakandare dake kasar.


Babban daraktan cibiyar bunkasa kimiyya da fasaha na Najeriya, Farfesa Okechukwu Ukwuoma, ne ya bayyana haka, yayin gabatar da jawabi a wurin wani taron bita da aka shiryawa masu bincike akan ilimi a garin Akure.

Farfesa Ukuoma ya ce tuni kwararru suka yi nisa wajen bincike tare da fassara jadawali da litattafan lissafi dana kimiyyar da daliban Najeriya zasu yi amfani da su zuwa harsunan gida.

A shekarar da ta gabata, Ma’aikatar Ilimi da ta Kimiyya da Fasaha suka kafa wani kwamiti da aka dorwa alhakin jagorantar shirin fara koyar da Lissafi da sauran darussan na kimiyya zuwa harsunan gida.
Rfihausa.

No comments:

Post a Comment